26 Agusta 2014 - 09:51
Japan za ta samar da maganin gwaji na Ebola

Gwamnatin kasar Japan ta ce za ta samar da maganin da ake gwajinsa, domin taimakawa wajen yaki da annobar Ebola a yammacin Afrika idan ana bukatar hakan.

Sai dai Hukumar lafiya ta Duniya ba ta amince da maganin na T-705 a hukumance ba, kuma babu tabbacin ko zai yi aiki wajen warkar da masu cutar Ebola.

Amma wani kakakin kamfanin hada magunguna na Toyoma Chemical ya ce yanayin cutar Ebola da kwayoyin cutar mura na kama da juna, don haka maganin zai yi aiki.

Kawo yanzu dai babu takamaimai maganin cutar ta Ebola, sai dai an samu nasarar warkar da wasu Amurkawa biyu da suka kamu da cutar da maganin Zmapp da ake gwajinsa. ABNA